Zaman farko na majalisar dokokin kasar Burma

Majalisar dokokin kasar Burma
Bayanan hoto, A karon farko tun bayan zaben da aka gudanar a kasar Burma, Majalisar dokokin kasar Burma zata soma wani zama daga yau
An wallafa

Sabbin 'yan siyasar da aka zaba a babban birnin kasar Burma da kuma takwarorinsu sojoji suma sababbi na wani zaman majalisar dokoki tare a karo na farko.

Jam'iyyar Union Solidarity and development party dai ita ke da rinjaye a sabuwar majalisar dokokin kasar wacce keda goyan bayan gwamantin mulkin soji mai ci yanzu.

Jam'iyyar ta USDP ta lashe kusan kashi 70 cikin 100 na kuri'un da aka kada a watan Nuwamba, zaben daya sha suka daga ciki da kuma wajen kasar.

Jam'iyyar dake goyan bayan Aung San Sui Kyi ta yanke shawarar kauracewa zaben.

Rahotanni sunce an tsaurara matakan tsaro a wajen harabar majalisar dokokin kasar.

Ba a kuma gayyaci 'yan jaridu dama ma'aikatan diflomaciya zuwa wajen gudanar da bikin bude sabuwar majalisar ba