Kamfanin Nokia na fuskantar baraza

Sabon shugaban kamfanin samar da wayar salula na Nokia, ya gargadi ma'aikatan kamfanin cewa kamfanin na cikin matsala.
Stephen Elop ya bayyana kamfanin a matsayin wanda ke zagaye da abokan hamayyarsa wadanda ke kokarin kwace masa kasuwa ta hanyar fasahar zamani.
A takaice, ya ce, kamfanin na cikin hadari kan nasarar da wayar Android ta Google da kuma iPhone ta Apple ke samu.
BBC ta tabbatar da ingancin wasikar da shugaban ya rubuta. "iPhone ta farko an kirkireta ne a 2007, kuma har yanzu ba mu da wayar da ta kama kafarta," a cewar Mr Elop a takardar da ya aika wa ma'aikatan kamfanin na kasar Finland kuma shafin intanet na Engadget ya wallafa.
Abin da mamaki
"Yayin da Android ta zo shekaru biyu kawai da suka wuce, kuma a wannan makon sun kwace mana ikon da muke da shi na samar da wayoyin hannu na zamani. Abin da mamaki.

Asalin hoton, BBC World Service
Duk da cewa Nokia ce kan gaba wajen sayar da wayoyi na zami, hannayen jarinta na ci gaba da ja baya.
Binciken da kamfanin IDC ya gudanar, ya nuna cewa darajar hannayen jarin Nokia sun fadi daga kashi 38% a 2009 zuwa kashi 28% a karshen 2010.
Yayin da abokan hamayyarta, da suka hada da Apple da HTC, hannayen jarinsu sun karu ko kuma sun tsaya yadda suke.
Ben Wood, wani masani a kamfanin bincike na CCS, ya ce wasikar ta nuna cewa Mr Elop ya san "irin matsalolin da ke damun kamfanin na Nokia".
A ranar Juma'a ne ake saran Nokia za ta bayyana matakan da za ta dauka nan gaba domin shawo kan matsalolinta a wani taron manema labarai.































