Takaddama tsakanin Fulani game da Jonathan

An wallafa

Wata takaddama ta kunno kai a tsakanin Fulanin da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya bayan wani gangami da wasu shuwagabannin Fulani na Jihohin dake yankin suka shirya domin nuna goyon bayansu ga Shugaba Goodluck Jonathan a zaben dake tafe.

Wadanda suka shirya taron, sun bayyana cewa Shugaba Jonathan ne zai kai kasar gaci.

Sun kuma bayyana cewa sun tuntubi Fulanin dake yankin kafin su gudanar da gangamin.

Sai dai kuma wasu Fulanin sun nesanta kansu da wannan taro suna masu cewa ba da yawunsu aka yi ba.