An kammala zaben shugaban kasa a Nijar

Zabe a Nijar
Bayanan hoto, Zabe zagaye na biyu a Nijar
An wallafa

An kammala kada kuri'a a zaben shugaban kasar jamhuriyar Nijar, zagaye na biyu.

Da misalin karfe shidda da rabi ne dai aka rufe rumfunan zaben a duk fadin kasar, a wannan zabe da ake fafatawa tsakanin Alhaji Seyni Oumarou na jam'iyyar MNSD- NASSARA, da Alhaji Mahammadou Issoufou na jam'iyyar PNDS Tarayya.

Zaben dai ya gudana lafiya, kuma rahotanni na cewa galibi dai jama'a sun fito domin kada kuri'unsu.

Dukkan 'yan takarar biyu dai sun yi alkawarin rungumar sakamakon zaben, wanda zai mayar da kasar ta Nijar bisa tafarkin demokradiyya, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a bara, sakamakon kiki-kakan siyasar da aka samu.