Sauyi ta fanin demokuradiyya a Najeriya

An wallafa
Najeriya na bukater ababen more rayuwa da kuma farfado da masana'antun da suka durkushe.
Bayanan hoto, Najeriya na bukater ababen more rayuwa da kuma farfado da masana'antun da suka durkushe.

A shekarar 1999 ne Najeriya ta sake komawa ga turbar demokuradiyya, a wani lokaci da `yan kasar ke cike da fatan cewa rayuwarsu za ta inganta.

Sai dai bayan sama da shekaru goma sha biyu da komawa ga wannan tafarki, `yan Najeriyar da dama na kukan cewa maimakon demokradiyyar ta kyautata rayuwarsu sai tagayyara suke yi, lamarin da ya cusa `yan kasar cikin tunanin ko zuwa yaushe ne za su samu sauyin da suke fata.

Ibrahim Isa ya yi nazarin irin matsalolin da ke hana demokuradiyya tasiri a Najeriya da kuma hanyar inganta ta. A yi sauraro lafiya.