Tattaunawa a kan sarandar Laurent Gbagbo

Asalin hoton, BBC World Service
A Cote d'Ivoire, bayan an kwashe kwanaki ana kazamin fada a birnin kasuwanci na Abidjan, ministan harkokin wajen Faransa, Alain Juppe, ya ce ana cigaba da tattaunawa game da ficewar mutumin da ya ki sauka daga mulki bayan faduwa zabe, Laurent Gbagbo, daga cikin kasar.
Mr. Juppe na magana ne jim kadan bayan da ministan hulda da kasashen waje na Mr. Gbagbo, Alcide Djedje, ya ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Ya ce, yanzu haka yana gidan jakadan Faransa, kuma tun jiya da misalin karfe sha daya na dare ya je can da izinin shugaba Laurent Gbagbo, domin kulla yarjejeniyar tsagaita bude wuta.
Ministan ya ce an cimma matsaya, don haka yakin ya kare.
Sai dai manyan kwamandojin da ke biyayya ga daya shugaban na Cote d'Ivoire, Alassane Ouattara, sun ce babu wata yarjejeniyar da za su amince da ita, muddin ba ta hada da sarandar Mr. Gbagbo ba tare da wani sharadi ba.



























