Kotu ta haramta jam'iyyar Hosni Mubarak

Asalin hoton, BBC World Service
An wallafa
Kotun kasar Masar ta bada umurnin rushe jam'iyyar National Democratic Party ta tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak.
Kotun kolin ta ce, a kwace dukkanin abubuwan da jam'iyyar ta National Democratic Party ta mallaka, wadanda suka hada da kudi da kadarori, kuma ta ce a mika su ga gwmanatin kasar.
Ana ganin wannan mataki a matsayin babbar sakayya ga wadanda suka yi zanga-zangar adawa da gwamnati, wadda ta yi sanadiyyar saukar shugaba Mubarak daga kan karagar mulki.
Wakilyar BBC ta ce, mutane sun fusata ne da jam'iyyar ta NDP, bayan zaben 'yan majalisar dokokin kasar da aka tabka magudi, wanda aka yi a watan Nuwambar bara.
Jam'iyyar ta NDP dai ta samu kashi tamanin cikin dari na kujerun 'yan majalisar da aka kada.






















