Tawagar majalisar dinkin duniya na ziyartar kasar Libya

An wallafa

Wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ta kai ziyara zuwa Tripoli, babban birnin kasar Libya ta fara gudanar da bincike a kan zargin tauye hakkokin bil adama a rikicin da kasar ke fuskanta.

Cherif Bassiouni dake jagorantar tawagar ya ce,yana da tambayoyi da dama a kan bama baman da aka jefawa fararen hula da azabtarwa da amfani da sojin haya da kuma tsare yan jarida na kasashen waje.

Gwamnatin libya dai ta ce za ta bayar da hadin kai ga masu binciken, amma ta jadada bukatar ganin cewa an binciki dukkanin bangarorin da rikicin ya shafa.

Peter Bouckaert jamii ne a kungiyar kare hakin bil adama ta Human Rights Watch kuma yayi wa BBC karin bayani a kan shawarar da kungiyarsa ta baiwa tawagar Majalisar Dinkin Duniyar:

Ya ce,"mun fada musu cewa su bi a hankali dangane da zargin fareren hula da suka mutu da gwamatin kanar Gaddafi ta yi saboda mun san cewa ana sauya bayanai".