An zargi sojoji da kashe mutane 11 a Maiduguri

Asalin hoton, 1
A Najeriya, wadansu mazauna birnin Maiduguri sun zargi jami'an rundunar hadin gwiwa ta tsaro wato JTF da kashe mutane goma sha daya wadanda suka ce galibinsu matasa ne ba tare da sun aikata wani laifi ba.
A ranar Asabar din da ta gabata ne dai jami'an JTF a Maidugurin suka sanar da cewa sun hallaka mutane goma sha daya wadanda suke zargin cewa 'yan kungiyar nan ce ta Jama'atul Ahalil sunnah Lidawati wal jihad wadda aka fi sani da Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno.
Sai dai Malam Dala Abacha, mahaifin wasu daga cikin mutanen da aka kashe, ya ce sojojin sun yi kutse cikin gidajensu ba tare da wani dalili ba inda suka kama 'yayansa:
''Ranar Juma'a da misalin karfe goma sha biyu da mintuna hamsin aka kwankwasa kofar gidana da na makocina, inda sojoji suka shiga suka tafi da yara na guda uku dana makotana guda tara.Mun ce su bamu yaran sai suka tafi da su, inda daga bisani suka kashe su''.
Sai dai rundunar JTF ta ce ta kashe mutanen ne a wata musayar-wuta da suka yi da su.






















