Ana maida martani kan abinda ke faruwa a Syria

Asalin hoton, BBC World Service
An wallafa
Kasar Tunisia ta ce zata kori jakadan Syria daga kasar a matsayin wani martani na abinda ta kira kisan kiyashin da akai a Homs.
Ta kuma ce baza ta kara daukar gwamnatin Syriar a matsayin gwamnati ba.
A Libya kuma wasu 'yan Syriar da sukai zanga zanga sun yi ta daga tutar 'yan adawa ta Syrian National Council akan ofishin jakadancin Syrian dake Tripoli.
Can kuma a Masar wani gungun masu zanga zanga ne suka farwa ofishin jakadancin Syrian, inda suka kakkarya kujeru da teburan suka kuma cinna wuta a wani sashe na ofishin.
Hakan nan ma an kai hare hare a ofisoshin jakadancin Syrian dake Kuwait da Jamus da kuma Girka.



























