An kashe mutane da dama a Aleppo na Syria

Harin da aka kai a Aleppo na kasar Syria
Bayanan hoto, Harin da aka kai a Aleppo na kasar Syria
An wallafa

Akalla bama bamai biyu sun fashe a birnin Alepoo dake Syriya.

Bama baman dai sun jawo asarar rayuka da jikkatar wasu da dama.

Gidan Talabijin na kasar ya ce akalla mutane ashirin da biyar sun mutu a harin, dari da saba'in kuma sun jikkata.

Jagoran sojin kwato yancin Syrian, Kanal Aref Alhamoud ya shaidawa BBC cewa dakarunsu sun kai hari kan dakarun tsaron Syria.

Amma kuma ya musanta cewa su ne suka kai harin bam din.