Ayarin motocin Shugaba Mugabe sun yi hadari

Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe
Bayanan hoto, Shugaban Zimbabwe, Robert Mugabe
An wallafa

Yan sanda a kasar Zimbabwe sun ce an halaka mutum guda sannan kimanin mutane goma sha biyar sun jikkata, a wani hadari wanda shugaban kasar Robert Mugabe ke ciki.

Yan sandan sun ce wata karamar motar safa ta ki kaucewa daga kan titi duk da jiniyar da ke kadawa, sannan ta yi karo da motar yan sanda.

Kakakin yan sandan bada kariya ga manyan masu mukamai, Martin Mbokochena ya dora alhakin hadarin akan wadanda ya bayyana da cewa masu adawa da ci gaban kasar.

Wannan dai shi ne karo na uku a cikin makonni biyu da wani ya rasa ransa a wani hatsari da ya ritsa da ayarin motocin shugaban kasa a Zimbabwe.