Boko Haram sun dau nauyin kai harin Plateau

Shekau
Bayanan hoto, Malam Abubakar Shekau
An wallafa

Kungiyar Jama'atu Ahlul sunnah lilda'awati wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram ta futar da wata sanarwa inda a ciki ta dauki nauyin hare-haren da aka kai a Barikin Ladi da Riyom a Jihar Plato.

Harin dai ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama har da Sanata da kuma dan majalisar Jihar.

Haka kuma sanarwar ta karyata batun tattaunawa da mai bawa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro ya ce zai yi da su.

Sanarwar dai ta yi gargadi ga Jamaar gari da su daina shiga cikin fadan da suke yi.

Kungiyar ta ce ta yi farin ciki da nasarar da ta samu na kai hare-hare a yankin Barikin Ladi da Riyom a Jihar Plato wanda hakan in ji sanarwar ya yi sanadiyyar mutuwar Kiristoci da jami'an tsaro har da Sanata da kuma dan majalisa duk daga Jihar ta Plato.