Ana tattaunawa tsakanin gwamnati da Azbinawa

Azbinawa a lokacin tattaunawar
Bayanan hoto, Azbinawa a lokacin tattaunawar
An wallafa

An soma tattaunawar sulhu tsakanin gwamnatin Mali da Azbinawa 'yan aware dake rike da garin Kidal mai matukar muhimmanci.

Shugaban Burkina Faso, Balise Compaore dake shiga tsakani a birnin Ouagadougou yayi kiran a kawo karshen fada tsakanin bangarorin biyu domin a samu damar gudanar da zaben shugaban kasar cikin watan gobe.

An dai gwabza fada sosai cikin 'yan kwanakin nan, yayin da dakarun gwamnatin Mali suke nausawa zuwa garin Kidal.

A shekara ta 2012 ne,i Azbinawa 'yan tawaye da masu kaifin kishin Islama suka kwace iko da mafi yawancin arewacin Mali kafin dakarun Faransa su taimaka wajen fatattakarsu.