Kalubale ga Dimokuradiyya a Masar

Mohammed Morsi
Bayanan hoto, Mohammed Morsi
An wallafa

Shugaban kasar Masar, Mohammed Morsi, ya yi gargadin cewar banbancin siyasa na yin barazana ga dorewar dimokuradiya a kasar.

A wani jawabi ga jama'ar kasa baki daya ta gidan talbijin na bukin cika shekara daya da hawa kan karagar mulki, Mr Morsi ya amsa cewa lalle ya tafka wasu kura-kurai.

To amma yayi kira ga masu adawa da su bayyana ra'ayinsu ta hanyar jefa kuru'a.

Masu goyan bayan Mr Morsi da kuma 'yan adawa na shirin gudanar da manya manyan gangami a wannan makon.

Wakilin BBC a Cairo ya ce duk da kalamai na neman sasintawa da suka fito daga Mr Morsi, jawabin yayi tir da wasu mutane da ya dora alhajin matsalolin Masar akansu.