Shari'ar addini da tsarin mulki a Amurka

An wallafa
Kotun kolin Amurka za ta yanke hukunci kan ko za a iya bude tarukan jama'a da addu'a ko kuma a'a.
Ana ganin shariar za ta iya shafar tanadin tsarin mulkin Amurka da ya raba harkar addini da ta gwamnati.
Wasu mazauna garin Greece da ke jihar New York, su biyu ne suka shigar da kara kan al'adar bude taro da addu'a, inda su ka ce hakan ya saba wa tsarin mulkin Amurkan wanda ya haramtawa gwamnati ta rungumi wani addini.
Mutanen biyu, daya bayahude daya kuma ba shi da addini, sun bukaci cewa in har za a yi wata addu'a a lokacin fara wani taro to kamata yayi addu'ar ta zama ba ta wani addini guda ba.
Amma kuma daya daga cikin alkalan da ke shari'ar ya ce abu ne mai wuya a gamsar da kungiyoyin addinai daban daban da addu'a daya.






















