An kashe dakaru fiye da 60 a Sudan ta Kudu

An kashe sojoji fiye da 60 lokacin bata kashi a cikin kwanaki biyu a Juba babban birnin kasar Sudan ta Kudu.
Wani likita a asibitin sojoji ya bayyana cewar tuni aka yi jana'izar dakarun da suka mutu.
Wani sabon rikici ya barke a ranar Talata kwana guda bayan da gwamanti ta ce ta murkushe yinkurin juyin mulki.
Rahotanni sun bayyana cewa fiye da mutane 100 ne suka jikkata, a daidai lokacin da hukumomin kasar ke kokarin shawo kan lamarin.
A ranar Litinin, Shugaba Salva Kiir ya zargi sojojin dake biyayya ga tsohon mataimakinsa, Riek Machar, wanda ya kora a watan Yuli.
Ministan harkokin wajen Sudan ta Kudu, Barnaba Marial Benjamin ya ce jami'an tsaro na fatattakar ragowar magoya bayan tsohon mataimakin shugaban kasar da ake zargi da shirya juyin mulkin.






















