Thailand: An hana 'yan takara rijista

Masu zanga zangar na adawa da shirin yin zaben da gwamnati ta shirya inda suke bukatar fraiministar ta sauka kawai.
Bayanan hoto, Masu zanga zangar na adawa da shirin yin zaben da gwamnati ta shirya inda suke bukatar fraiministar ta sauka kawai.
An wallafa

Masu zanga zangar adawa da gwamnati sun yi wa wani filin wasa a babban birnin Thailand, Bangkok inda 'yan takarar zaben kasar na watan Fabrairu za su yi rijista, kawanya.

Masu zanga zangar suna adawa da zaben, wanda Pirai minista Yingluck Shinawatra ta shirya sakamakon manyan zanga zanga da ake yi na neman ta sauka daga mulki.

Su na zanga zangar ne kwana daya bayan da jam'iyyar adawa ta Democrat Party ta ce ba za ta shiga zaben na watan Fabrairun ba, matakin da masu zanga zangar ke cewa yayi daidai.

Wani mai zanga zangar ya ce ya yadda da shawarar 'yan jam'iyyar ta Democrat, ta kauracewa zaben saboda idan suka shiga zaben jam'iyyar za ta mutu murus, kuma ba za ta taba dawowa ba.