CAR: An fillewa yara kanana biyu kai

Mutane dubbai sun fice daga gidajensu a Bangui
Bayanan hoto, Mutane dubbai sun fice daga gidajensu a Bangui
An wallafa

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiran da a gaggauta daukar matakin kare kananan yara a jamhuriyar Tsakiyar Afrika, saboda ana fillewa yara kanana kai.

Rikici tsakanin kungiyoyin 'yan banga Musulmi da Kirista yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu daya a cikin wata guda da ya wuce.

Asusun tallafa wa kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi gargadin cewa hare-haren da ake kaiwa yara kanana na daukar wani sabon salo, na tsagwaron rashin imani, -- inda yanzu haka akwai kananan yara biyu da aka datse wa kai, wani yaran kuma aka yi gunduwa gunduwa da shi.

Kungiyar ta ce ana kai hare-hare a kan yara da niyyar ramuwar gayya.

Bayan haka kuma ana daukar su a matsayin mayaka a rikicin jamhuriyar tsakiyar Afrikar, wanda ya yi sanadiyar raba mutane kusan dubu 400 da muhallansu, a Bangui, babban birnin kasar.