Al Shabab ta haramta intanet a Somalia

Dakarun Al Shabaab na kashe wadanda su ke zargi da leken asiri.
Bayanan hoto, Dakarun Al Shabaab na kashe wadanda su ke zargi da leken asiri.
An wallafa

Kungiyar masu kishin Islama ta Al Shabab - wacce ta mamaye mafi yawan kudanci da tsakiyar Somalia - ta haramta amfani da intanet a yankunan da take iko.

Kungiyar mai alaka da Al Qaeda ta bai wa kamfanonin sadarwa wa'adin kwanaki 15 su toshe hanyoyin shiga intanet.

Al Shabab ta ce za ta dauki duk wani kamfani ko mutum da bai yi aiki da dokar ba a matsayin wanda ke hada baki da makiyanta.

Al Shabab dai na yawan kashe mutanen da ta yi zargi da yi wa gwamnatin Somalia ku kuma Turawan Yamma leken asiri.