Fulani sun koka kan kisan mummuke

Fulani makiyaya suna korafi kan rikice-rikice
Bayanan hoto, Fulani makiyaya suna korafi kan rikice-rikice
An wallafa

A Najeriya, kungiyar makiyaya ta miyetti Allah ta koka a bisa abinda ta kira matsalolin da makiyaya ke fuskanta a kasar.

A cewar kungiyar a cikin watanni biyar kadai, an hallaka makiyaya fiye da dari uku baya ga asarar Shanu sama da dubu goma.

Kungiyar dai ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyar kasar da ta dauki matakin gudanar da bincike don hukunta duk wadanda ke da hannu wajen halaka makiyaya da sace musu Shanu.

Ana yawaitar samun rikice-rikice tsakanin fulani da makiyaya a sassa daban-daban na kasar.