Fyaɗe na ƙaruwa a Kano

Asalin hoton, BBC World Service
An wallafa
Rahotanni daga Kano a arewacin Najeriya na cewa, ana samun ƙaruwar aikata fyaɗe, inda lamarin ya fi shafar yara mata ƙanana.
Koda a yau an gaurfanar da wani matashi a gaban kotu bisa zargin yiwa wata yarinya 'yar shekaru biyar fyaɗe a makon da ya gabata.
Hukumomin jihar ta Kano na cewa matsalar ta fyaɗe a kullum ƙaruwa take yi, ganin yadda ake samun ƙaruwar waɗanda ake gurfanarwa a gaban kotu.
Jihar Kano dai tana cikin jihohin arewacin Najeriya da ake aiwatar da shari'ar musulunci.



























