Gwamnonin Arewa za su gana

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto, Arewacin Najeriya na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro
An wallafa

A Najeriya, a yau ne ake saran gwamnonin arewacin kasar za su gudanar da wani taro a Kaduna,domin duba abinda suka ce matsalolin da ke addabar yankin.

Ana tsammanin batutuwan da suka shafi tabarbarewar harkar tsaro da kuma koma bayan tattalin arzikin yankin idan aka kwatanta shi da sauran yankunan kasar ne zasu mamaye tattaunawar.

Al'ummomin arewacin kasar dai na fatan cewa taron zai kasance mabudin warware matsalolin yankin musamman a wannan karo da matsalolin ke kara ta'azzara.

Ko a ranar asabar da daddare sai da wasu 'yan bindiga suka halaka mutane sama da 100 a jahar Bornon Najeriyar baya ga kashe kashen da aka yi a jahar Adamawa.