Rasha za ta taimaka a sako sojojin Turai

Asalin hoton, AP
Wakilin Rasha a kungiyar tsaro da hadin kan Turai ya ce kasarsa za ta yi duk abinda ya dace wajen ganin an sako jami'an sojin Turai da aka tsare a gabacin Ukraine.
Jami'an sojin da kuma wasu hafsoshin sojin Ukraine da dama ne wasu magoya bayan Rasha suka tsare a ranar Juma'a a birnin Sloviansk.
Shugabannin kasashe bakwai masu arzikin masana'antu sun ce za su kara kaimin takunkumi akan Rasha dangane da rikicin na Ukraine.
Kasashen dai na zargin Rasha ne da jagorantar tawayen da magoya bayan ke yi a gabacin Ukraine.
Sanarwar tasu ta zo ne a lokacin da ake cigaba da tsare jami'an sojin Turan a gabacin kasar ta Ukraine.
Wani shugaban dakarun dake goyon bayan Rasha dai ya ce za a yi musanyarsu da sojin sa-kai din da Ukraine ta tsare.
Firaministan wucin-gadin kasar Ukraine, Arseniy Yatsenyuk, ya zargi Rashan da haddasa fitina a duniya.
Yace: "A fili take cewa tsokanar fadan da Rasha ke yi nada manufar lalata harkokin tsaro da zaman lafiya na duniya, domin canja taswira da kuma juya abubuwan da yakin duniya na biyu ya haddasa."
Rasha dai ta musunta zargin na shi, sojojinta kuma sun ci gaba da yin atisaye domin shirya wa abinda ka biyo baya.


























