An yi ruwan kifi a Sri Lanka

An wallafa
Mutanen karkara a arewacin kasar Sri Lanka sun ce sun yi matukar mamaki da kuma murna bayan da aka yi musu ruwan kifaye --lamarin da ba su saba gani ba.
Ana tsammanin iska ce ta rika dauko kifayen daga wani kogi tana watso su cikin garuruwa lokacin da ake yin ruwa ranar Litinin .
Wasu mazauna karkara sun ce sun rika jin karar wasu abubuwa na sauka, kuma da suka duba sau suka ga fiye da kilogram na kananan kifaye a gidajensu.
Wannan dai ba shi ne karon farko da ake yin ruwan kifaye a Sri Lanka ba; a shekarar an yi ruwan kifaye a wasu wurare na kudancin kasar.






















