'Chibok: Sojojin Nigeria sun kawar da kai'

Jihar Borno na karkashin dokar ta-baci.
Bayanan hoto, Jihar Borno na karkashin dokar ta-baci.
An wallafa

Kungiyar Amnesty International ta ce an kwarmatawa sojojin Nigeria batun kai hari a makarantar Chibok, tun kafin a kai harin, amma kuma suka ki daukar mataki.

Wasu majiyoyi masu karfi sun shaidawa Amnesty International an sanarda da dakarun soji a Maiduguri babban birnin jihar Borno sa'o'i hudu tun kafi a kai harin.

Dalibai fiye da 53 ne suka kubuce a yayin da akwai sauran fiye da 200, har yanzu a hannun 'yan Boko Haram din.

Tawagar kwararru daga Amurka da Birtaniya sun isa Nigeria don taimakawa wajen gano inda 'yan matan suke domin a ceto su.

'Rashin Makamai'

Uwargidan Shugaban Amurka, Michelle Obama ta bi sawun masu neman a sako 'yan matan.
Bayanan hoto, Uwargidan Shugaban Amurka, Michelle Obama ta bi sawun masu neman a sako 'yan matan.

A cewar Amnesty duk da gargadin da aka bayar, sojojin sun ki tura jami'an tsaro don kare makarantar da ke kauyen Chibok a jihar Borno.

Kungiyar ta ce watakila sojojin sun ki daukar mataki ne "ba suda manyan makaman tunkarar Boko Haram".

Ana zargin cewar an kai 'yan matan dajin Sambisa da ke makwabtaka da jamhuriyar Kamaru.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce za su sayar da 'yan matan a kasuwa.

An kiyasta cewar 'yan Boko Haram sun kashe mutane fiye da 1,200 a wannan shekarar ka dai.