An kama wani mutum kan harin Brussels

Asalin hoton, Reuters
An wallafa
'Yan sanda a Faransa sun kama wani mutum da ake zargi da kashe mutane akalla uku a harin da aka kai da bindiga a watan da ya wuce a wani gidan kallo na Yahudawa a birnin Brussels.
A cewar 'yan sandan, mutumen mai shekaru 29, an yi amunnar ya je Syria a bara tare da masu jihadi.
An kama shi ne a birnin Marseilles, na kudancin Faransar, yayin da yake sabka daga wata motar bus ta haya.
'Yan sandan sun ce yana dauke da bindiga kirar Kalashnikov da kuma wata karamar bindigar, masu kama da wadanda aka yi amfani da su wajen harin na Brussels.
Shugaban Faransar, Francois Hollande, ya ce zasu yi iya kokarinsu su tabbatar cewa masu jihadin basu yi barna ba a duk inda suke.



























