Samsung ta fitar da sabuwar waya

sabuwar wayar Tizen da kamfanin Samsung ya kirkiro a kokarinsa na ci gaba da zama jagora tsakanin sauran kamfanonin waya.
Bayanan hoto, sabuwar wayar Tizen da kamfanin Samsung ya kirkiro a kokarinsa na ci gaba da zama jagora tsakanin sauran kamfanonin waya.
An wallafa

Kamfanin kayan laturoni na Samsung ya kaddamar da wayar salula tasa ta farko mai manhajar komai-da-ruwanka .

Kamfanin ya ce ya kirkiro da wayar ce mai manhajar da ya kira Tizen (Samsung Z a takaice) domin ya daina amfani da manhajar Android ta kamfanin Google.

Za a fara sayar da wayar ta Samsung Z a Rasha tsakanin watannin Yuli zuwa watan Satumba.

Yawanci wayoyin Samsung na amfani da manhajar Andriod amma kamfanin na Korea ta kudu ya hada hannu da kamfanin Intel don kirkiro da manhajar ta Tizen.

Hakan dai wata hanya ce da kamfanin Samsung zai rage amfani da manhajar Andriod ta Google.

Mataimakin shugaban kamfanin Frost & Sullivan Andrew Milroy ya bayyana wa BBC cewa, "Manhajar za kuma ta bai wa Samsung damar dara sauran abokan hamayyarsa.

Sai dai kuma ba a ganin cewa matakin na Samsung zai haifar da faduwar kasuwar Android.

Kamfanin Samsung zai ba je kolin wayar a taron da za a gudanar a wannan mako a San Francisco, sai dai kamfanin bai bayyana farashin wayar ba.

Shagon Tizen

Yanzu haka Samsung ke kan gaba a duniya wajen sayar da wayoyi masu dauke da manhajar Andriod.

Koda yake dai sauran kamfanoni da suka hada da HTC da Sony da LG da Huawei su na amfani da tsarin manhajar ta Android.

Yayin da ake ci gaba da gasa tsakanin kamfanoni wayoyin komai-da-ruwanka Samsung ta himmatu wajen neman hanyoyin ci gaba da kasancewa jagaba a kasuwar.

Daya daga cikin hanyoyin da Samsung ta maida hankali shine kirkiro Tizen.