Masu fafutuka sun karbe iko da Mosul

Wasu dakarun Iraqi
Bayanan hoto, Masu fafutukar dai a baya sun karbe iko da wasu garuruwa a kasar
An wallafa

Masu tsattsauran ra'ayin Islama sun karbe iko da gine-ginen gwamnati a Mosul, gari na biyu mafi girma a Iraqi.

Jami'ai sun ce masu fafutukar na kungiyar kafa daular Musulunci a Iraqi da sham sun saki daruruwan fursunoni, yayin da kuma suka karbe iko da filin jiragen saman birnin.

Rahotanni sun ce sojoji da 'yan sanda sun gudu, haka ma dubban mazauna birnin na tserewa, hatta gwamnan lardin shi ma rahotanni na cewa ya tsere.

Kakakin majalisar dokokin kasar ya ce birnin na Mosul ya koma hannun 'yan ta'adda, kuma ya nemi gwamnati ta tura karin dakaru da gaggawa.