Minista: Majalisa ta amince da Shekarau

Wata guda kenan da shugaban kasar ya mika sunayensu ga majalisar
Bayanan hoto, Wata guda kenan da shugaban kasar ya mika sunayensu ga majalisar
An wallafa

Majalisar dattawan Nigeria ta tabbatar da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim shekarau a matsayin minista.

Sauran wadanda aka tabbatar a matsayin sababbin ministoci, a gwamnatin shugaba Goodluck Jonathan sun hada da Abdul Bulama daga jihar Yobe da Adedayo Adeyeye daga jihar Ekiti da kuma Stephen Oruh daga jihar Delta.

Majalisar ta amince da hakan ne a zamanta na ranar Laraba, bayan sun bayyana a gabanta kuma ta tantance su.

Nan gaba ne ake sa ran shugaban kasar zai bayyana ma'aikatun da za su rike.