HRW: Sojin Kenya sun aikata ta'asa

Jami'an tsaron Kenya
Bayanan hoto, Jami'an tsaron Kenya
An wallafa

Kungiyar kare hakkin bil Adama ta Human Rights Watch ta ce rundunar yaki da ta'addanci ta Kenya tana aikata ta'asa a gaban idanuwan gwamnati da ofisoshin jakadancin kasashen yamma da kuma na Majalisar Dinkin Duniya.

Rundunar yaki da ta'addancin na samun tallafin kudaden gudanar da ayyukan ta ne daga kasashen Amurka da Burtaniya. An kafa sashen ne a shekarar 2003 shekaru biyar bayan wasu hare hare a jere da al-Qa'ida ta kai ofisoshin jakadancin Kenya da Tanzania.

Mutane fiye da 200 ne suka hallaka a harin da ya kasance mafi girma da al-Qa'ida ta kai a wancan lokaci.Kasashen na Kenya da Amurka da kuma Burtaniya basu maida martani ba tukunna a kan rahoton kungiyar kare hakkin bil Adaman ta HRW

Kungiyar ta zayyana kisan kai guda goma da aukuwar tilasta bacewar mutane a lokuta daban daban har sau goma da kuma laifuka goma sha daya cin zarafin mutanen da ake zargi da ayyukan ta'addanci galibi a Nairobi babban birnin kasar a shekarar 2011.

" Akwai bukatar kasashe masu bada agaji su gudanar da nasu binciken wadannan cin zarafi su kuma dakatar da tallafin da suke baiwa sojojin da ke cin zarafin al'umma ko kuma a zarge su da hadin kai da al'adar rashin hukunta jami'ai da ke amfani da matsayinsu wajen cin zarafin al'umma wanda kasar Kenya ta yi kaurin suna a kai, a cewar kungiyar ta HRW".