Syria: Fada ya sake barkewa a Kobane

Garin Kobane na kasar Syria
Bayanan hoto, Garin Kobane na kasar Syria
An wallafa

Fada ya sake barkewa a titunan garin Kobane na kasar Syria, yayinda mayakan IS suka shiga gabashin garin makonni 3 da yi masa kawanya.

Sa'o'i bayan da aka daga wasu tutoci 2 na kungiyar ta IS a gefen garin, masu fafutika na Syria da kuma rahotannin yankin sunce an soma yakin kwanton baunar a birane.

Wani jami'in Kobane ya shaidawa BBC cewar Kurdawa za su rike wurin na tsawon lokaci saboda dakarun kungiyar IS ba za su iya amfani da tankokin yakinsu ko kuma wasu manyan makamai a matsatstsun tituna ba.

Daruruwan Kurdawan Syria ne ke tserewa daga garin,wandake kusa da kan iyakar Syriar da Turkiyyar.