Canada ta dauki mataki kan Ebola

Asalin hoton, EPA
An wallafa
Kasar Canada ita ce kasa ta biyu da ta soke bawa dukkan mutanen da suka fito daga kasashen yammacin Afurka da cutar Ebola ta fi kamari Bisar shiga cikinta.
Gwamnatin kasar ta ce ba za a ba mazauna kasashen da 'yan kasar da Ebolar ta addaba damar shigowa Canadar ba.
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO tace rufe iyakokin kasashe ba zai hana cutar Ebola yaduwa ba.
Har yanzu kasashen Guinea da Laberia da kuma Saliyo su ne inda Ebola tafi kamari.



























