China ta musanta rufe shafukan Internet

Shafin sada zumunta na Facebook
Bayanan hoto, Facebook na daya daga cikin shafukan da aka rufe a kasar ta China.
An wallafa

Daraktan da ke kula da shafukan kasashen waje na Internet a kasar China yace ba za a iya bude wasu daga shafukan ba, sai dai ya musanta cewar an rufe shafukan baki daya.

Lu Wei wanda shi ne shugaban ofishin watsa labarai ta Internet yace ofishin sa na shirin sake daukar wasu karin matakai a shafukan Internet.

Ba a iya bude shafukan Twitter da Facebook da New York Times a kasar ta China.

Ko a farkon watan Oktoba da ya wuce an rufe shafin turanci na BBC a China.

Mr Lu dai na amsa tambayoyi ne a wajen wani taro gabannin fara babban taron yanar gizo na duniya da za a yi a yankin Zhejiang na kasar.

Ko da manema labarai suka tambaye shi dalilin da ya sanya ake rufe shafuka irinsu Facebook, Mr Lui kada baki ya yi yace bai taba amfani da irin wadannan shafuka ba dan haka shi ma bai san dalilin da ya sanya aka rufe su ba. Amma idan an tambaye shi dalilin da ya sa ba a iya ziyarar wasu shafukan Internet yana da amsar ba da wa.

Ya kuma kara da cewa ''Ba mu taba rufe wani shafin Internet na kasar waje ba, abin nan fa a gidan ku yake. Ta yaya zan je har gidajen ku na rufe su''?

Mr Lu ya ce matakan da ofishinsa ya dauka don kare muradu da kuma ayyukan jami'an tsaron China ne.

Ana tsaurara matakai matuka a shafukan Internet na kasar China, kuma duk wani abu da za a wallafa da ta shafi sukar gwamnati ba abari a shafukan na Internet.

Inda ko a baya-bayan nan ma ba a cika barin abubuwan da aka wallafa da suka shafi boren da aka yi a Hong-Kong ba a shafin Internet na kasar wato Weibo.