Nawaz Sherif ya yi martani kan kisan kiristoci

An zargi mamatan ne da wulakanta Alkur'ani mai tsarki
Bayanan hoto, An zargi mamatan ne da wulakanta Alkur'ani mai tsarki
An wallafa

Firai ministan Pakistan, Nawaz Sherif, ya bayyana kisan wasu ma'aurata Kirista da wasu Musulmi suka yi a matsayin muguntar da ba za a amince da ita ba.

A ranar Talata ne aka yi wa mutanen biyu dukan-kawo-wuka har suka mutu, a wani karamin gari da ke da nisan kilomita sittin daga birnin Lahore.

Mr. Sherif ya ce gwamnati ba za ta amince mutane su dauki doka a hannunsu ba.

Hakan ya biyo bayan wata zanga-zanga da kiristoci 200 suka yi a birnin Lahore, suna kira da ayi garonbawul kan dokar batanci na kasar.