An kara ta'adi a kamfanin simintin Ashaka

'Yan Boko Haram sun ce sun kafa daular musulunci
Bayanan hoto, 'Yan Boko Haram sun ce sun kafa daular musulunci
An wallafa

Wasu mahara da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan garin Bajoga da ke jihar Gombe inda suka kona ofishin 'yan sandan garin.

Mazauna garin dai sun ce sun ji karar harbe-harbe da abubuwa masu fashewa, lamarin da ya sa dubban jama'a gudun tsira.

Bayanai sun ce 'yan Boko Haram din sun bayyanawa fararen hula cewar ba wurinsu suka zo ba.

Daga garin Bajoga, 'yan Boko Haram din sun shiga cikin kamfanin siminti na Ashaka inda suka yi harbe-harbe.

Wanda ya shaida lamarin ya ce "Maharan sun shiga cikin ma'aikatar siminti, sun je dakin ajiye nakiyoyi amma basu samu ko mai ba."

"Sun je asibiti sun tafi da motar asibiti da kuma magunguna kafin jiragen saman yaki na soji suka kawo dauki," in ji ma'aikacin kamfanin siminti na Ashaka.

A watan jiya ma 'yan Boko Haram sun kai farmaki a masana'antar siminti ta Ashaka da ke jihar ta Gombe, kuma sun yi awon-gaba da nakiyoyin da ake fasa duwatsu da su.