Kungiyar kwadago na so a rage farashin mai

Mr Jonathan ya kara kudin man fetur lamarin da ya sa aka yi zanga-zanga a Najeriya
Bayanan hoto, Mr Jonathan ya kara kudin man fetur lamarin da ya sa aka yi zanga-zanga a Najeriya
An wallafa

Kungiyar kwadago ta Najeriya, NLC ta bukaci gwamnatin kasar ta rage farashin man fetur.

Kungiyar ta ce hakan ya zama wajibi ganin cewa farashin man fetur ya fadi a kasuwar mai ta duniya.

Sai dai wasu masu sharhi a kan al'amuran tattalin arziki na cewa, ba lallai ne gwamnati ta rage kudin man ba, saboda har yanzu ba a soke tsarin bayar da tallafin mai ba a kasar.

A shekarar 2012 ne dai shugaban kasar Goodluck Jonathan ya kara kudin man fetur daga N65 zuwa N97, lamarin da ya jawo zanga-zanga a kasar.

Najeriya dai tana cikin kasashen kungiyar da ke samar da man fetur na duniya amma 'yan kasar na fama da matsanancin talauci.