Kungiyar MSF za ta janye daga Sudan

Ana fama da fari a yankuna da dama na Sudan
Bayanan hoto, Ana fama da fari a yankuna da dama na Sudan
An wallafa

Kungiyar agajin likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce za ta janye tawagarta daga Sudan saboda hukumomi a kasar suna mata katsalandan da gangan a yankunan da ake tashin hankali.

MSF ta ce gwamnatin Sudan na amfani da wasu dabaru wajen hana ta kai wa wasu yankunan da ke jihohin Darfur da kuma Blue Nile.

A jihohin dai akwai dubban mutanen da ke bukatar kayayyakin agaji.

Dakarun Sudan na yaki a yankunan da ke kan iyakar kudancin kasar domin murkushe ayyukan 'yan tawaye.

A makon da ya gabata ne MSF ta zargi dakarun sojin saman Sudan da wurga bambamai a wani asibiti da ke tsaunin Nuba.