Venezuela: An zargi magajin-gari da shirya juyin mulki

An yi awon gaba da magajin garin babban birnin Caracas
Bayanan hoto, An yi awon gaba da magajin garin babban birnin Caracas
An wallafa

Masu gabatar da kara a Venezuela sunce su na wani shiri na tuhumar magajin garin Caracas, babban birnin kasar, bisa hannu a wani shiri na hanbarar da gwamnati.

An tsare Antonio Ledezma wanda dan siyasa ne na bangaren 'yan adawa a ranar Alhamis, bayan wasu mutane sanye da kakin soji sun kutsa kai cikin ofishinsa ta karfin tsiya.

Shugaban Kasar Venezuelan Nicolas Maduro ya zargi Amurka da hannu a shirin hanbarar da gwamnatinsa.

Sai dai Wani mai magana da yawun fadar White House ya ce babu gaskiya a zarge zargen.