Sojojin Congo sun kashe 'yan tawayen Rwanda

Asalin hoton, AFP
An wallafa
Gwamnatin Jamhuriyar dimokuradiyyar Congo ta ce sojojinta sun kashe 'yan tawayen Rwanda akalla bakwai sun kuma kama wasu ashirin a wani sabon samame da suka kai a gabashin kasar.
Wani mai magana da yawun gwamantin ya ce an kashe 'yan tawayen ne, wadanda 'yan kungiyar FDLR ta 'yan kabilar Hutu ne, a samamen da aka kai a lardunan Arewaci da Kudancin Kivu.
Ya ce mayakan kungiyar 'yan tawayen ta FDLR sun gudu sun bar akasarin makamansu.
Kungiyar ta FDLR ce dai ummul haba'isin tashe-tashen hankula a gabashin Congo tun bayan da 'yan kabilar Hutu suka ketare iyaka bayan kisan kare dangi na Rwanda a shekarar 1994.



























