'Yan ci-rani 800 sun isa Indonesia

Daruruwan 'yan cirani sun sha mutuwa a teku a tafiyar da suke yi mai cike da hatsari
Bayanan hoto, Daruruwan 'yan cirani sun sha mutuwa a teku a tafiyar da suke yi mai cike da hatsari
An wallafa

Kimanin 'yan cirani 800 sun isa Indonesiya bayan wasu jiragen kamun kifii sun ceto su a lokacin da jirginsu ya nutse a cikin teku.

Rahotanni sun ce sojojin ruwan Indonesiyan sun umarci wani jirgin ruwa dauke da 'yan cirani ya koma bayan ya yi yunkurin shiga cikin ruwan kasar.

Wadanda ke cikin jirgin ruwan na cikin dubban 'yan ci-rani daga Rohinja da Bangaladesh, wadanda suka shafe makonni a teku bayan an ki ba su izinin sauka a kasashen Malaysia da Indonesiya.

Wani jirgin ruwan kuma da wakilin BBC ya shiga a tekun Thailand a yanzu ya ci gaba da tafiya, bayan da sojoji suka shiga cikin jirgin, suka gyara injinsa.

Jami'ai sun ce a yanzu shi ma wannan jirgi ya tunkari Indonesiyan.

Wakilin BBC ya ce da dama daga cikin wadanda ke cikin jirgin na bukatar kulawa ta lafiya, bayan shafe kusan watanni uku a cikin teku ba tare da isashen abinci ko ruwa ba.