Amnesty ta zargi Hamas da gallaza wa Palasdinawa

Shugaban kungiyar Hamas, Khaled Meshaar
Bayanan hoto, Shugaban kungiyar Hamas, Khaled Meshaar
An wallafa

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, ta zargi kungiyar Hamas ta Palasdinawa da laifin azabtarwa da sace wa da kuma kisan farar hula Palasdinawa a Gaza, a lokacin da suka yi fito-na-fito da Isra'ila a bara.

Kungiyar ta Amnesty ta dauki hotuna sama da 20 na abinda ta kira kashe-kashen da aka yi ba tare da wata shari'a ba.

Amnesty ta ce wadanda aka azabtar din 'ya'yan kungiyar Fatah ne ta Palasdinawa.

Ta kuma kara da cewa abin kunya ne ace a dai-dai lokacin da Isra'ila ke kai hare-haren da ke hallaka farar hula masu dimbin yawa, Hamas kuma tana amfani da wannan damar wajen ramuwar gayya a kan wasu masu adawa da ita.