An kashe mai shigar-da-kara a Masar

Asalin hoton, AP
An wallafa
Mai gabatar da kara na kasar Masar, Hisham Barakat, ya mutu sakamakon raunukan da ya ji bayan wani harin bom na mota da aka kai a birnin Alkahira.
An kai harin ne kan jerin gwanon motocin da Mr Barakat ke ciki a lokacin da suke kan hanya a lardin Heliopolis.
Karfin fashewar ya lalata motoci da shaguna da dama.
Masu tsaron lafiyar Mr Barakat biyu su ma sun samu raunuka.
Mr Barakat ya sha kai dubban masu kaifin kishin Islama gaban kuliya, tun bayan da sojoji suka hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi a shekara ta 2013.
Wata kungiya da ba a san ta ba sosai da ake kira ''Popular Resistance of Giza'' ta ce ita ce ta kai harin.






















