'El-Rufai yana nada bare a kan mukamai'

El Rufai na shan suka da wadanda suka taya shi cin zabe.
Bayanan hoto, El Rufai na shan suka da wadanda suka taya shi cin zabe.
An wallafa

Wasu 'yan jam'iyyar APC a jihar Kaduna da ke Najeriya sun yi zargin cewa gwamna Malam Nasir El-Rufai yana nada bare mukamai.

Masu sukar gwamnatin dai na yin hakan ne ganin nadin da gwamnan ya yi wa Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar ma'aikata ta gwamna da Muyiwa Adeleke a matsayin mai bayar da shawara na musamman kan watsa labarai.

Kazalika, 'yan jam'iyyar ta APC sun ce gwamnan bai gaya musu cewa zai nada wadanda ba 'yan jihar ba ne a kan mukaman siyasa lokacin da yake yakin neman zabe.

Sai dai a nata martanin, gwamnatin El Rufai' ta ce cancanta ta sa aka nada mutanen a kan mukaman, tana mai cewa baya ga haka, dukkan su a jihar ta Kaduna aka haife su.