Biritaniya na son fara luguden wuta a Syria

An wallafa
Ministan tsaron Burtaniya zai bada shawarar cewa majalisar dokokin kasar ta sake duba matakin data dauka na kin amincewa da kaiwa mayakan IS a Syria hare- hare
Ana tsammanin Michael Fallon, zai fadawa 'yan majalisar dokokin cewa babu ma'ana ga Burtaniyan ta shiga cikin hare- haren da ake kaiwa mayakan IS a Iraqi, amma banda idan an tsallaka kan- iyaka
Mr Fallon yace akwai yiwuwar cewa harin da mayakan IS din suka kaiwa wasu masu yawon bude ido 'yan Burtaniya a Tunisia a makon daya gabata, an shirya shine a birnin Raqqa na Syriar
'Yan majalisar dokokin Burtaniyan sun kada kuri'ar kin amincewa da kai hare- haren sama a Syriar shekaru biyu da suka gabata, amma yanzu an sami sabuwar gwamnati






















