An kai harin bam a Zaria

Asalin hoton, BBC World Service
An wallafa
Rahotanni daga Zaria da ke jihar Kaduna a Najeriya na cewa an kai harin bam a birnin ranar Talata.
Rahotannin sun ce ana zargin 'yan kunar bakin wake ne suka kai harin a lokacin da ake tantance ma'aikata a sakateriyar karamar hukumar Sabon Gari.
Har yanzu dai babu cikakken bayani a game da harin da kuma yawan mutanen da ya shafa.
A baya mutanen da ake zargi 'yan Boko Haram ne sun sha kai hare-hare a birnin.






















