An samu mai shafin intanet na Grooveshark a mace

An samu gawar, Josh Greenberg, daya daga cikin masu shafin kade-kade na intanet mai suna Grooveshark wanda kuma a ka rufe a baya bayan nan.
'yan sanda sun ce an ga gawar mamacin ne a gidansa da ke Florida.
Sai dai 'yan sandan sun ce ba bu alamun makarkashiya dangane da mutuwar ko kuma alamun kisan kai.
Josh Greenberg mai shekaru 28 ya kirkiri shafin kade-kade na Grooveshark ne a 2006.
Kuma a watan Aprilun shekarar 2015 ne a ka rufe shafin saboda jerin kararraki kan keta hakkin mallaka da shafin ya yi a lokacin gina rumbun kade-kaden nasa.
Hakan ne ya sa wata kotu a Amurka ta yanke hukuncin cewa shafin zai biya tarar tsabar kudi har dala miliyan 736.
Yanzu haka dai, mahaifiyar Josh Greenberg, Lori ta ce dan nata ya kasance cikin koshin lafiya saboda haka mutuwar tasa ta zo ma ta da bazata.

Su ma abokan aikin mamacin suna ta faman bayyana alhininsu dangane da rashin Josh, ta kafar sada zumunta ta Twitter.


























