Obasanjo da Jonathan sun gana da Buhari

Dr Goodluck Jonathan da Chief Olusegun Obasanjo
Bayanan hoto, Dr Goodluck Jonathan da Chief Olusegun Obasanjo
An wallafa

Fadar shugaban Nigeria ta tabbatar da cewa wasu tsofaffin shugabannin kasar biyu sun kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadar gwamnatin kasar.

Rahotanni sun ce a karshen makon da ya gabata ne dai tsohon shugaban kasar Dr Goodluck Jonathan ya ziyarci shugaba Muhammadu Buhari, yayin da shi ma tsohon shugaba Chief Olusegun Obasanjo ya ziyarci shugaba Buharin a ranar juma'ar data gabata.

To sai dai mataimaki na musammman ga shugaban kasa kan yada labarai Malam Garba Shehu ya ce ganawar sirri tsofaffin shugabannin suka yi da shugaba Muhammadu Buhari.

Ya kuma musanta cewa ziyarar wani mataki ne na neman shugaba Muhammadu Buhari ya sassauta a yakin da gwamnatin sa ke yi da cin hanci da rashawa.

Kungiyoyin da ke yaki da cin-hanci a Najeriya sun ce sun samu kwarin-giwa daga dukufar da gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma Amurka suka yi wajen binciko wadanda suka wawure kudaden kasar a shekarun baya.