'An kusa soma shari'ar barayin gwamnati'

Kwamitin ya gana da Buhari da kuma Jonathan kafin zaben 2015
Bayanan hoto, Kwamitin ya gana da Buhari da kuma Jonathan kafin zaben 2015
An wallafa

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ce nan da wasu 'yan makonni za a soma shari'ar mutanen da suka sace dukiyar kasa.

Shugaban ya bayyana haka ne a ganawar da ya yi da 'yan kwamitin wanzar da zaman lafiya wanda Janar Abdussalami Abubakar ke jagoranta.

Shugaban Buhari ya kara da cewa bayan gwamnati ta nemi a mai do da irin kudaden da aka sace aka kai bankunan kasashen waje, za kuma ta tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda suka sace irin wadannan kudade a gaban kuliya.

"Mun ci baya a cikin 'yan shekarun nan a matsayinmu na kasa, shi ya sa muke cikin matsalar tattalin arziki da kuma tsaro!" In ji Buhari.

A nasa bangaren, tsohon shugaban mulkin sojin kasar, Janar AbdulSalami Abubakar ya bukaci shugaba Buhari ya tabbatar da bin doka da oda a kokarinsa na yaki da cin hanci da rashawa.