Liberia ta kawar da cutar Ebola

Wani mutum da ya warke bayan ya kamu da cutar ebola
Bayanan hoto, Wani mutum da ya warke bayan ya kamu da cutar ebola
An wallafa

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana Liberia a matsayin kasar da ta kawar da cutar ebola baki daya a karo na biyu.

A watan Mayun da ya gabata ne ta ce kasar ta kawar da kwayar cutar ta ebola baki daya , sai dai daga bisani an samu wani da ya kamu da cutar a watan Yuni.

Hukumar lafiyar ta ce za a karfafa sa ido a kan ko za a sake samun wani da ya kamu da cutar a cikin kwanaki 90 masu zuwa.

Kasashen Guinea da Saliyo da ke makobtaka da Liberia kawo yanzu na samun mutanen da ke kamuwa da cutar ta ebola.